Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai Ya Caccaki Donald Trump
(last modified Sat, 15 Sep 2018 11:21:47 GMT )
Sep 15, 2018 11:21 UTC
  • Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai Ya Caccaki Donald Trump

Shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar tarayyar turai Jean-Claude Junker ya caccaki shugaban kasar Amurka Donald Trump dangane da matsalolin da yake ta haifar wa duniya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da rahoton cewa, a jawabinsa da ya gabatar a zaman shekara -shekara da majalisar kungiyar vtarayyar turai take gudanarwa  a birnin Brussele s na kasar Belgium, Jean-Claude Junker ya bayyana cewa dole ne kungiyar tarayyar turai ta mike tsaye domin tabbatar da sahihan manufifinta  aduniya.

Jean-Claude Junker ya ce ba zai yiwu wani ya fifita maslahar kasarsa a kan sauran dukkanin kasashen duniya ba, yana mai ishara da irin matakan da Trump ke dauka na takura kasashen duniya, inda ya ce tarayyar turai tana da shirin ganin ta nuna wa duniya sabbin tsare-tsarenta domin ci gaban duniya da kuma warware matsaloli masu tarin yawa da aka haidar tun bayan da Trump ya dare kan kujerar shugabancin Amurka.

Haka nan kuma Jean-Claude Junker ya bayyana ficewar Trump daga yarjejeniyar Paris ta dumamar yanayi da cewa abu ne mai hadari, haka nan kuma kara kudaden haraji ga kayayyakin kamfanonin kasashen duniya da ake shigar da su Amurka, da kuma haifar da yakin kasuwanci, gami da ficewar da ya yi daga yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran, inda shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar tarayyar turai Jean-Claude Junker ya ce dole ne a mike domin a tunkari wannan lamari.