Putin: Harin Da Isra'ila Ta Kai Siriya, Keta Hurumin Kasar Ne
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewar hare-haren da haramtacciyar kasar Isra'ila take kai wa kasar Siriya keta hurumin kasar Siriya yana mai, yana mai jan kunnen Isra'ilan da ta guji duk wani abin da zai sanya rayuwar sojojin Rashan da suke Siriya cikin hatsari.
Shugaba Putin ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da ta hada shi da firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ilan Benjamin Netanyahu wanda ya buga masa don kwantar da hankalin kasar Rashan kan kakkabo jirgin sojanta da aka yi a sararin samaniyyar kasar Siriyan.
Har ila yau dangane da harbo jirgin saman sojin na Rasha kuwa, shugaba Putin ya dora alhakin hakan kan sojojin haramtacciyar kasar Isra'ilan yana mai cewa kasar Rashan tana da hakkin mayar da martani kan hakan, kamar yadda kuma ya kirayi gwamnatin Netanyahu da ta guji ci gaba da keta hurumin kasar Siriya da kai hare-hare cikin kasar.
A jiya ne dai firayi ministan HKI Benjamin Netanyahun ya buga wa shugaban Rasha waya don ba da hakuri da kuma neman sasantawa dangane da harbo jirgin sojin Rashan da makamai masu linzamin sojojin Siriya suka yi a lokacin da suke kokarin harbo wasu jiragen yakin Haramtacciyar kasar Isra'ilan da suka shigo cikin kasar da nufin kai hari suna masu fakewa da jirgin sojin Rashan da aka kakkabo din a lardin Latakia na kasar Siriyan.