Faransa : Macron, Zai Gana Da Rohani A Babban Taron MDD
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai gana da takwaransa na Jamhuriya Musulinci ta Iran, a daura da babban taron Majalisar Dinkin Duniya, karo na 73 a birnin New York.
Wata sanarwa da fadar Elysee ta fitar a yau, ta ce Mista macron zai gana da Donald Trump a ranar 24 ga watan Satumba, zai kuma gana da shugaba Hassan Rohani a ranar 25 ga watan.
Daga cikin batutuwa da Macron zai tattauna da Donald Tromp, da akwai batun zurga zurga jiragen ruwa na tsakanin Amurka da Turai, da halin da ake ciki a Siriya da kuma matakan da Amurka ke dauka kan Iran.
A ganawar da zai yi da takwaransa na Iran, Dakta Hassan Rohani kuwa, Macron zai jaddadawa Iran mahimmancin ci gaba da kasancewarta a yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da ita, duk da ficewar Amurka.
A daya bangaren kuma, fadar Elysee ta ce tana ci gaba da tattaunawa da Iran, kan batun nada jakadanta a birnin Tehran.