Tarukan Ashura A Wasu Daga Cikin Biranen Kasashen Duniya
Daruruwan musulmi mabiya mazhabar ahlul bait ne yanzu haka suke gudanar da tarukan Ashura a birnin Madrid fadar mulkin kasar Spain.
Rahotanni daga birnin Madrid sun habarta cewa, tun a safiyar yau ne dimbin musulmi mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) suke gudanar da tarukan tunawa da zagayowar lokacin shahadar Imam Hussain a ranar Ashura.
A birane daban-daban na kasashen turai an gudanar da irin wadannan taruka, da suka hada da birane daban-daban na kasashen Birtaniya, Amurka, Jamus, Belgium, Canada, Australia, Holland, da sauransu.
A kasashen Asia da dama da suka hada da Malatysia, Pakistan, Afghanistan, Thainland, Indonesia, Turkiya, Rasha, India da dai sauransu ana gudanar da wadannan taruka.
A kasashen nahiyar Afrika da dama ma ana gudanar da irin wadannan taruka, da suka hada da Najeriya, Tanzania, Ghana, Mali, Senegal, Kamaru, Togo, Afirka ta Kudu, Uganda, Kenya, Zambia, Masar da sauransu.
A gabas ta tsakiya kuma ana ci gaba da gudanar da wadannan taruka a kasashen Iran, Yankunan Gabashin Saudiyya, Kuwait, Bahrain, Iraki, Yemen da kuma Lebanon.