MDD Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ahwaz
(last modified Sun, 23 Sep 2018 06:44:23 GMT )
Sep 23, 2018 06:44 UTC
  • MDD Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ahwaz

Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai garin Ahwaz dake kudu maso yammacin kasar Iran

Cikin wani jawabi da ya fitar a daren jiya assabar saktare janar na MDD António Guterres ya nuna alhininsa ga gwamnati da al'umma gami da iyalan wadanda harin ta'addancin ya ritsa da su, sannan ya bayyana fatan samun lafiya ga wadanda suka jikkata.

A safiyar jiya assabar ne kungiyar ta'addancin Al-ahwaziya dake samun goyon bayan mahukuntar biranan Riyad da Landon sun bude wuta kan jami'an tsaron Iran da fararen hula da suke gudanar da bikin makon tsaron kasa a garin Ahwaz da ke shiyar kudu maso yammacin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da kawo yanzu ya yi sanadiyar shahadar mutane 29 da kuma raunana wasu 57 na daban

Kawo yanzu dai kasashe da dama da suka hada da Rasha, Birtaniya, Oman, Yemen, Jamhoriyar Azarbajan, Pakistan, Afganistan, Siriya, Turkiya , Iraki sun yi Allah da wannan hari na ta'addanci, sannan kuma sun meka sakon ta'aziyarsu ga gwamnati da al'ummar kasar Iran da iyalen wadanda lamarin ya rusa dasu da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka raunana.