Amnesty Ta Yi Allawadai Da Tsare Dubban Mutane A Habasha
(last modified Tue, 25 Sep 2018 15:51:00 GMT )
Sep 25, 2018 15:51 UTC
  • Amnesty Ta Yi Allawadai Da Tsare Dubban Mutane A Habasha

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amesty International, ta yi allawadai da da cafke dubban mutane a Addis-Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.

A sanarwra data fitar, kungiyar ta ce tsare mutanen, barazana ce ga sabon babin fannin kare hakkin bil adama karkashin gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed.

Wata kafar radiyo kusa da gwamnatin kasar ta ce mutum 3,200 aka cafke. 

A kwanan nan ne dai hukumomin Habasha suka sanar da gudanar da gagarimin samame bayan rikicin kabilanci na tsakanin al'ummar Oromos da kuma wasu gungun kabilu wanda ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a babban birnin kasar da kuma kewayensa.

Wata majiya data bata so a bayyana sunanta ba, ta shaida wa kamfanin dilancin labaren faransa na AFP, cewa mutane 65 ne aka kashe a rikicin kabilancin.