Shugaba Maduro Ya Zargi Gwamnatin Amurka Da Kokarin Kashe Shi
(last modified Fri, 12 Oct 2018 05:34:14 GMT )
Oct 12, 2018 05:34 UTC
  • Shugaba Maduro Ya Zargi Gwamnatin Amurka Da Kokarin Kashe Shi

Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro, ya zargin gwamnatin Donald Trump ta Amurka da kokarin kashe shi yana mai bayyana aniyarsa ta kare kansa daga wannan makirci na Amurkan.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar shugaba Maduro ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi wa ma'aikatan kasar inda ya ce: gwamnatin Amurkan ta ba da umurnin a kashe shi, to sai dai ya sha alwashin cewa lalle ba za su iya cimma wannan aniya ta su ba.

Shugaban na Venezuela ya bayyana cewar gwamnatin Amurkan tana yakar ne ta hanyar matsin lamba na tattalin arziki da take yi wa kasar tasa, yana mai kore zargin da Amurkawan suke masa da takurawa 'yan adawa da hana su fadin albarkacin bakinsu, inda ya ce Amurkan ce take goyon bayan 'yan adawan wajen kashe shi ko kuma yi masa juyin mulki.

Fadar White House ta Amurka din dai ta musanta wannan zargin tana mai cewa siyasar Amurka a Venezuelan ita ce kokarin tabbatar da demokradiyya ta hanyar ruwan sanyi a kasar.