Amurka Ta Soke Atisayen Soji Da Koriya ta Kudu
(last modified Sat, 20 Oct 2018 11:02:27 GMT )
Oct 20, 2018 11:02 UTC
  • Amurka Ta Soke Atisayen Soji Da Koriya ta Kudu

Ministocin harkokin wajen kasashen Amurka dana Koriya ta Kudu, sun sanar da soke atisayen sojin hadin guiwa na tsakanin kasashen da aka shirya yi a watan Disamba mai zuwa.

Wannan dai wani mataki ne karfafa tattaunawa kan shirin nukiliyar Koriya ta Arewa.

Ministocin biyu sun ce wannan wata dama ce ta baiwa mahukuntan Pyongyang, duk wata dama ta ci gaba da tattaunawa kan shirinta na nukiliya a cewar kakakin ma'aikatar tsaron Amurka.

Duka dai wannan na daga cikin shirin sake yin wata tattaunawa ta kud da kud tsakanin shugaba Donald Trump na Amurka da kuma takwaransa na Kim Jong Un bayan wacce akayi a ranar 12 Yuni a Singapoor.