Canada Ta Bayyana Shirinta Na Dakatar Da Sayawarsa Saudiya Makamai
Piraministan kasar Canada ya bayana shirin kasarsa na dakatar da yarjejjeniyar sayar da makamai ga kasar Saudiya
A yayin da Duniya ke ci gaba da matsin lamba da kuna jin kunan mahukuntan birnin Riyad game da kisan dan jaridar nan mai sukan manufofin hukumomin Saudiya Jamal Khashoggi, Piraministan kasar Canada Justin Trudeau ya ce matukan dai kasarsa za ta samu tabbacin cewa Saudiya na mumunan amfani da makaman da ta sayar mata to shakka babu za ta fice daga yarjejjeniyar da suka kula na sayarwa saudiyar makamai.
A shekarar 2014 kasar ta Canada ta kulla yarjejjeniya ta Saudiya na sayar mata da makamai na dala biliyan 13.
Trudeau ya bayyana fatansa na cewa ana amfani da makaman da suka sayar bisa dokoki da kare hakin bil-adama.