Kasashen Spain Da Rasha Sun Yi Watsi Da Sharuddan Amurka
(last modified Tue, 06 Nov 2018 17:58:00 GMT )
Nov 06, 2018 17:58 UTC
  • Kasashen Spain Da Rasha Sun Yi Watsi Da Sharuddan Amurka

Ministocin harkokin wajen kasashen Spain da Rasha sun soki siyasar Amurka musamman kan takunkuman data sake kakaba wa Iran, tare da yin allawadai da sharudan da Amurka ta gindaya kan kasashen dake ci gaba da yin hulda da Iran din.

Bangarorin biyu sun bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ministan harkokin wajen Rasha, Sergueï Lavrov ya kai a birnin Madrid yau Talata.

Mista Lavrov ya bayyana cewa lokacin barazana da matsin lamba a wannan zamani ya wuce, kuma ba abun da za'a iya lamunta dashi ba ne.

Shi ma ministan harkokin wajen Spain din Josep Borrell, ya ce na goyan bayan takwaransa na Rasha akan kin amuncewa da duk wata barazana ba.

A jiya ne Amurka ta sake dawo da dukkan jerin takunkumanta kan Iran da suka hada da bangaren makamashi da da sufiri da kuma harkokin bankuna.

Amurkar dai ta yarde wa kasashe takwas kawai su ci gaba da sayan man fetur da Iran na akalla tsawan watanni shida, tare da cewa duk kasashe da kamfanonin dake son ci gaba da huldar kasuwanci da Amurka su daina hulda da Iran.