Amurka Zata Janye Sudan Daga Jerin Kasashen Dake Goyan Bayan Ta'addanci
(last modified Thu, 08 Nov 2018 16:02:33 GMT )
Nov 08, 2018 16:02 UTC
  • Amurka Zata Janye Sudan Daga Jerin Kasashen Dake Goyan Bayan Ta'addanci

Amurka ta ce a shirye take domin wajen aiwatar da shirin janye kasar Sudan daga cikin jerin kasashen dake goyan bayan ta'addanci.

Hakan dai a cewar mahukuntan na Washington ya biyo bayan da kasar ta Sudan ta fara cika alkawulan data dauka na bada hadin kai wajen yakar ta'addanci, da kare hakkin bil adama da 'yancin walwala da addini da kuma na fadar albarkacin baki da dai saurensu.

Saidai Amurkar ta ce tana jiran ta ga mahukuntan na Khartoum, su kara yi da gaske akan tabbatar da tsarin demukuradiyya. 

A shekara 1993 ne aka sanya Sudan a cikin jerin kasashen dake goyan bayan mayakan dake ikirari da sunan jihadi, bayan da jagoran kungiyar Al-Qaïda Usama Ben Laden ya rayuyi zama a kasar daga shekara daga 1992 zuwa 1996.

Bayanai sun nuna cewa dangantaka na dada farfadowa tsakanin Amurka da Sudan, bayan da a watan Oktoba na 2017, Amurkar ta janye mata da jerin takunkumai wanda hakan ya taimaka wa kasar wajen farfadowar tattalin arzikinta.