Nov 15, 2018 11:49 UTC
  • Britania Da Tarayyar Turai Cimma Yerjejeniya Kan Ficewar Britania Daga Kungiyar

Ministan harkokin waje na kasar Jamus ya yi maraba da cimma yerjejeniya wanda Britaniya da Tarayyar Turai suka yi.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli na kasar Turkiya ya nakalto Haeiko Mass yana fadar haka ya kuma kara da cewa kasar Jamus tana fatan zata ci gaba da hulda mai kyau da kasar Britania bayan ficewarta daga tarayyar ta Turai.

A nata bangaren fraiministan kasar Britania Theresa May ta bayyana a jiya Laraba kan cewa majalisar ministocinta ta amince da yerjejeniyar da suka cimma da tarayyar ta Turai. Sannan a yau Alhamis ne zata yi wa majalisar cikekken bayani na yerjejeniyar. An fara tattaunawa tsakanin Tarayyar ta Turai da Britania kan shirin ficewar daga tarayyar Turai wacce ake kira "Brexit" tun watan Maris na shekara ta 2017, kuma tana da lokaci har zuwa watan maris na shekara mai zuwa don kammala tattaunawar.

Tags