Kungiyar AU Na Gudanar Da Taro A Birnin Adis Ababa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34143-kungiyar_au_na_gudanar_da_taro_a_birnin_adis_ababa
A wannan Lahadi ne Kungiyar tarayyar Afirka ta fara gudanar da taron kwanakin uku a hedkwatar kungiyar dake birnin dis Ababa na kasar Habasha.
(last modified 2018-11-18T19:02:05+00:00 )
Nov 18, 2018 19:02 UTC
  • Kungiyar AU Na Gudanar Da Taro A Birnin Adis Ababa

A wannan Lahadi ne Kungiyar tarayyar Afirka ta fara gudanar da taron kwanakin uku a hedkwatar kungiyar dake birnin dis Ababa na kasar Habasha.

A yayin Buda taron, Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya bukaci shugabannin kasashen Afirka da su gaggauta amincewa da bukatun kawo sauyi kan yadda ake tafiyar da kungiyar kasashen Afirka .

Kagame yace lokaci yayi da za’a sake fasalin kungiyar ta zama mai dogaro da kanta, maimakon wadda ta dogara ga taimako daga kasashen duniya da kuma bata karfin fada aji kan duk wasu matsalolin da suka shafi nahiyar.

Shugaban Rwanda dake kamala wa’adin sa na shugabancin kungiyar a watan Janairu mai zuwa yace a karon farko kungiyar ta samu nasarar kaddamar da asusun zaman lafiya da zai dinga kai dauki mai kunshe da Dala miliyan 400.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewar wasu kasashen Afirka na dari dari da shirin kungiyar na katsalandan domin sasanta rikicin da ake samu a cikin mambobin kungiyar, abinda basa sa goyan bayan shirin na shugaba Kagame.