Canada Ta Sanya Wa 'Yan Saudiyya 17 Takunkumi
Kasar Canada, ta sanar da sanya takunkumin hana shigar kasar, ga wasu 'yan Saudiyya 17 da ake zargi da hannu a kisan dan jaridan nan Jamel Khashoggi a ranar 2 ga watan Oktoba da ya gabata a karamin ofishin jakadancin Saudiyyar na Santambul.
Da take sanar da hakan ministar harkokin wajen Canada, Chrystia Freeland, ta ce Takunkuman sun hada da toshe kaddadorin mutanen da kuma hana su shiga kasar.
Mutanen dai da gwamnatin Otawa ta sanya wa wannan takunkumin sun hada da wasu makusantan yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammad ben Salmane, da kuma jami'an Saudiyyar da suka shiga Turkiyya don kashe dan jaridan dake sukan manufofin masarautar Saudiyyar.
Kasar ta Canada dai ta ce bata gamsu ba da bayannan da Saudiyyar ta bayar ba kan kisan dan jaridan, tare da bukatar a gudanar da bincike mai zurfi domin gano suwa keda hannu a kisan na Jamel Khashoggi.
A cewar dai kafofin yada labarai da dama na Amurka, hukumar leken asiri ta Amurka CIA, yarima mai jiran gado na Saudiyyar ne, MBS, ya bada umurnin kashe dan jaridan, saidai har yanzu masarautar ta Saudiyya na ci gaba da musanta hannun yariman a cikin kisan.