Rahoton UNICEF Kan Kasashen Da Rayuwar Yara Ke Cikin Hadari
Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya fitar da wani rahoto dangane da kasashen da rayuwar yara tafi fuskantar hadari.
Kamfanin dillancin labaran ISNA ya bayar da rahoton cewa, a mafi yawan lokuta kasashen da ake fama da yaki ko kuma wasu rikice-rikice ko matsaloli na tsaro rayuwar yara tafi fadawa a cikin hadari.
Rahoton ya ce a cikin watanni 12 da suka gabata, kasashen da rayuwar kananan tafi zama cikin hadari a duniya su ne: Afghanistan, Yemen, Iraki, Syria, Myanmar, gabashin Ukraine, Kamaru, Sudanta kudu, Afrika ta tsakiya, Chadi, Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, Somalia, Najeriya, Nijar, da kuma yankunan da ke kan iyaka tsakanin Mali da Burkina Faso.
Rahoton ya kara da cewa, yara da suke rayuwa a yankuna da ake fama matsaloli na tsaro a cikin wadannan kasashe, su ne suka fi fuskantar matsala, baya ga matsaloli na tsaro, a wasu yankunan ma sukan fuskanci matsaloli na yunwa da karancin kayayyakin kiwon lafiya.