Paparoma Yayi Gargadi Ga Kasashen Duniya Kan Yiyuwan Awkuwar Yakin Duniya
(last modified Tue, 08 Jan 2019 06:55:25 GMT )
Jan 08, 2019 06:55 UTC
  • Paparoma Yayi Gargadi Ga Kasashen Duniya Kan Yiyuwan Awkuwar Yakin Duniya

Paparoma Francis shugaban mazhabar Catholica ta kiristoci ya yi gargadi ga shuwagabannin kasashen duniya da su yi hattara don kada su jawo yakin duniya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana haka ne a jiya Litinin, a lokacinda yake ganawa da jakadun kasashen waje a birnin Vatican .

Paparoma Francis ya ce yadda tashe-tashen hankula suka yadu a duniya a halin yanzu ne, ya sa yake jan kunnen kasashen duniya kan yiyuwar hakan ya kai ga yakin duniya na ukku. 

Paparoman ya bukaci kasashen duniya su rungumi tattaunawa da fahintar juna a duk sabanin da ta taso a tsakaninsu don kaucewa yake-yaken da ke lashe rayukan mutane a yankuna daban -daban a halin yanzu a duniya.

Dangane da bakin haure kuma Paparoman ya ce lamarin bakin haure ya zama abin bakinciki a duniya a halin yanzu. A nan ya bukaci kasashen duniya su mutunta yerjeniyoyin da suka cimma kan bakin haure.

Daga karshe ya bukaci a mutunta baki yan gudun hijira a karbesu kamar yadda dokokin kasa da kasa suka danaja, ko kuma a maidasu kasashensu tare da mutunci da kuma girmamawa.