A kwai shakku kan ajiya makamai a kasar Cote D'ivoire
Korarru a Majalisar Dinkin Duniya sun Bayyana shakku kan yiyuwar karbe makamai daga hanun wasu Matasa a kasar Cote D'ivoire
A wata sanarwa da ta fitar yau, tawagar kwararu na MDD a kasar Cote D'ivoire ta bayyana cewa a rikicin zaben shekarar 2010-2011 na kasar kimanin ton uku na makamai ne 'yan adawar Gwamnati da wasu 'yan tawaye suka saya a kasar ta Cote D'ivoire, ita dai wanda tawaga ta MDD mai kumshe da kwararu biyar ta fara gudanar da bincekenta ne tun a watan yunin shekarar baya a kasar ta cote D'ivoire.
Rahoton ya ce a kwai shakku na yiyuwar meka dukkanin wadannan makamai ga hanun gwamnati, da kuma hakan shi ke sanya fargabar sake billar wani rikici a kasar
Tawagar kwararrun ta wallafa wannan sakamako ne tun kafin ta gabatar da shi a zauren Kwamitin tsaro na MDD.