Faransa Ce, Ke Talauta Afrika, Inji Italiya
Ministan tattalin arzikin kasar Italiya, Luigi di Maio, ya zargi kasar Faransa da zama ummul'aba'isin talaucin dake addabar kasashen Afrika.
Mista Maio, ya ce kamata ya yi kungiyar tarrayyar turai ta kakaba wa Faransa dama sauren kasashe kamar Faransar dake talauta Afrika takunkunmi, wanda hakan ne yake sa mutanen Afrikar barin kasashensu, saboda a cewarsa kamata ya yi 'yan AFrika su zauna Afrika, ba wai a tekun mediteranien ba.
Ya kara da cewa, idan mutanen Afrika suna barin kasashensu a yau, saboda kasashen turai, musamman faransa, har yanzu bata daina mulkin mallakar gomman kasashen Afrika ba ne, sannan ya ce ba dan Afrika ba, Faransa bata isa ta zo a jerin kasashe shida mafiya tattalin arziki ba, saidai ta zo ta 15.
Wadannan kalamman ministan na Italiya sun janyo babbar muhawara kan shafukan sada zumunta musamman tsakanin 'yan AFrika, wadanda dama suka jima suna nuna sukan siyasar Farnasa a Afrika.
Tuni dai kasar Faransa ta kira jakadan Italiya a kasar, bayan da ministan na Italiyar, ya firta wadannan kalamman.
Kafin hakan dama wasu manyan jami'an Italiya na ci sukan siyasar Faransa, musamman kan batutuwan da suka shafi kwararar bakin haure da kuma nuna goyan baya ga bore da al'ummar kasar Faransa ke yi a baya bayan ta kin jinin gwamnatin shugaba Macron saboda wasu matakan gwamnatinsa da suka ce na takurawa masu karamin hali ne.