Talauci A Afrika : Faransa Ta Yi Tir Da Kalamman Italiya
(last modified Wed, 23 Jan 2019 11:14:02 GMT )
Jan 23, 2019 11:14 UTC
  • Talauci A Afrika : Faransa Ta Yi Tir Da Kalamman Italiya

Kasar Faransa ta kira jakadiyar Italiya a kasar, domin nuna masa bacin ran ta dangane da kallaman ministan tattalin arzikin Italiyar, na cewa Faransa ce silan talauci a Afrika

Wasu majiyoyin diflomatsiyya Faransa da kamfanin dilancin labaren Italiya ya nakalto, sun ce kalamman ministan na kin jinin faransa, basu da tushe, duba da huldar dake tsakanin kasashen biyu, a kungiyar tarayya Turai.

Shi dai ministan tattalin arzikin kasar Italiya, Luigi di Maio, ya zargi kasar Faransa ne da zama ummul'aba'isin talaucin dake addabar kasashen Afrika.

Mista Maio, ya ce kamata ya yi kungiyar tarrayyar turai ta kakaba wa Faransa dama sauren kasashe kamar Faransar dake talauta Afrika takunkunmi, wanda hakan ne yake sa mutanen Afrikar barin kasashensu, saboda a cewarsa kamata ya yi 'yan AFrika su zauna Afrika, ba wai kulun kan tekun mediteranien ba.

Ya kara da cewa, idan mutanen Afrika suna barin kasashensu a yau, saboda kasashen turai, musamman faransa, har yanzu basu daina mulkin mallakar gomman kasashen Afrika ba ne, sannan ya ce ba dan Afrika ba, Faransa bata isa ta zo a jerin kasashe shida mafiya tattalin arziki ba, saidai ko ta zo a matsayi na 15.

Wadannan kalamman ministan na Italiya sun janyo babbar muhawara kan shafukan sada zumunta musamman tsakanin 'yan Afrika, wadanda dama sun jima suna sukan siyasar Faransa a Afrika.