Sojojin Venezuela Sunyi Wa Trump Raddi
Sojojin Venezuela, sunyi wa shugaba Donald Trump na Amurka raddi, akan furucin da ya yi na basu zabin, ko dai su goyi bayan jagoran ‘yan adawa Juan Guaido ko kuma su rasa samun afuwa.
Akan ne sojojin na Venezuela suka maida masa da martanin cewa suna ci gaba da goyan bayan halataccen shugaban kasar Nicolas Maduro.
A hannu guda kuma kan cewar da shugaba Trump ya yi na cewa abu ne mai yiyuwa Amurka ta yi amfani da kowacce dama a kan kasar, sojojin kasar sunce a shirye suke na kalubalantar duk wani yunkuri na keta iyakokin kasar.
Trump dai ya bayyana hakan ne a yayin jawabi wani jawabinsa gaban magoya bayansa da kuma ‘yan asalin kasar Venezuela mazauna birnin Miami, inda yake cewa wadanda suka goyi bayan Guaido za a yi musu afuwa domin ci gaba da rayuwa tare da iyalansu, wadanda suka ki kuwa za su yi da na sani.
Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin shugaba Maduro ta hana shigo da kayayyakin agaji daga Amurka , a yayin da shi kuwa Mista, Guaido ya gargadi gwamnatin Maduro da ta bayar da hanyar shigo da kayayyakin agajin nan da ranar Asabar mai zuwa.
Mista. Guaido wanda kimanin kasashen duniya hamsin a sahun gaba Amurka ke mara masa baya na ci gaba da kallon kansa a matsayin shugaban kasar Venezuela na riko, a yayin da shi kuwa shugaba maduro ke ci gaba da watsi da barazanar kasashen da matsin lambar da suke masa na kira zabe, lamarin da ya kara dagula rikicin siyasar kasar.
Kasashen Rasha, China, Turkiyya da kuma Iran, na ci gaba da allawadai da abunda suka kira shishigi a cikin al'amuran cikin gida na Venezuela, maimaikon neman hanyar sansanta 'yan kasar akan rikicin siyasa.