Feb 20, 2019 17:48 UTC
  • Takunkumin Tarayyar Turai Akan Kasar Rasha

Kungiyar Tarayyar Turai ta kakaba sabbin takunkumai akan kasar Rasha saboda sabani akan mashigar ruwan Kerch

Kamfanin dillancin labarun Sputnik ya kara da cewa; Takunkumin ya kuma shafi kara wa'adin tsohon takunkumin akan wasu fitattun 'yan kasar Rasha su 8.

Jami'ar harkokin siyasar waje da kuma tsaro ta tarayyar turai Federica Maria Mogherini ce ta sanar da kakaba takunkumi wanda ta danganta shi da abin da ya faru a mashigar ruwan Kerch

A ranar 25 ga watan Nuwamba na 2018 ne aka yi taho mu gama a tsakanin jiragen ruwan Rasha da na kasar Ukraine a mashigar ruwan Kerch. Tarayyar turai ta nuna goyon bayanta ga kasar Ukraine wacce take kokarin zama memba a cikin kungiyar.

Mashigar ruwan Kerch ce kadai hanyar da jiragen ruwan Ukraine suke amfani da ita domin isa zuwa tasoshin jirage ruwa biyu na kasar

Tags