Amurka Za Ta Sanyawa Venezuela Karin Takunkumi
Feb 25, 2019 10:15 UTC
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fada a jiya Lahadi cewa Amurka za ta sanya karin takunkumi kan kasar Venezuela.
Akwai wasu karin takunkumai da za'a sanya, in ji Pompeo a tattaunawarsa da gidan talabijin na CNN.
Mataimakin shugaban kasar Amurka ya bayyana hakan ne gabanin tashinsa zuwa jihar Colombia domin halartar taron gungun kasashen Lima Group.
Taron na Lima Group, wanda ya kunshi kasashe 13 na yankin Latin Amurka da Canada, zai tattauna ne game da halin da ake ciki a kasar Venezuela.
Kasashen China, Rasha da kuma Iran na zargin Amurka da shishigi a cikin al’amuran cikin gida na kasar ta Venezuela.
Tags