Kasashen Gungun Lima Sun Kalubalanci Amfani Da Karfi A Venezuela
Gungun kasashen Latine Amurka na Lima dake adawa da mulkin shugaba Nicolas Maduro, sun kalubalanci duk wani yunkuri na yi amfani da karfi kamar yadda Amurka take shirin yi a kasar Venezuela.
Kasashen 14 mambobin gungun na Lima, sunyi kira da a samar da wata hanya ta mika mulki ta hanyar demokuradiyya a wannan kasar ta Venezuela, tare da cwa su al'ummar ta Venezuelar ne zasu zama wa kansu abunda suke so.
Saidai duk da hakan kasashen sun ammanar cewa ana fama da mawuyacin hali a kasar ta Venezuela.
Amurka dai ta ce zata iya daukar duk wani mataki kan shugaban kasar ta Venezuela, Nicolas Maduro, ciki kuwa harda yiwuwar amfani da karfi.
Kasashen da suka hada da China, Rasha da kuma Iran, na ci gaba da yin tir da yadda Amurka ke kokarin kifar da gwamnatin Nicolas Maduro, tare da danganta lamarin da shishigi na wuce gona da iri.