Mar 12, 2019 04:13 UTC
  • Duniya Na Kauracewa Amfani Da Jiragen Sama Kirar Boeing 737 MAX 8 Na Amurka

Tun bayan hatsarin jirgin sama na Ethiopian Airlines da ya faru a ranar Lahadi data gabata a Adis Ababa na kasar Habasha, wasu kamfanonin jiragen sama suka fara kauracewa ko kuma dakatar da amfani da jiragai na kamfanin kera jiragen sama na Amurka Boeing samfarin 737 MAX 8.

Kasar China wacce ta fara daukan matakin ta bukaci dukkan kamfanonin jiragen sama na kasar, dasu dakatar da zurga zurga da da samfarin jirgin na Boeing 737 MAX 8.

Matakin ya biyo bayan hatsarin da jirgin saman fasinja na Ethiopian Airlines 737 MAX 8, ya yi a jiya Lahadi, wanda kuma ya hallaka dukkan mutane 157 dake cikinsa, jim kadan bayan tashinsa daga Adis Ababa.

Dama kafin hakan irin hakan ta taba faruwa ga wani jirgin kamfanin Indonusia na Lion Air , wanda shi ma ya fado jin kadan bayan tashinsa a cikin watan Oktoban bara inda dukkan fasinjoji 189 dake cikinsa suka rasa rayukansu.

A cikin sanarwar da hukumar kula da sufurin jiragen sama fasinja ta China ta fitar, ta ce daukan wannan matakin wanda zai fara aiki daga yammacin yau Litini, na daga cikin karfafa tsaro a harkokin sufirin al'umma na jiragen sama.

Sanawar ta kara da cewa, an dau matakin har sai mahukuntan Amurka dana kamfanin jiragai na Boeing sunyi karin haske.

Hukumomin na China sun yi la'akari ne da hatsarurukan da jiragen samfarin Boeing 737 MAX 8, wadanda sabbin hutowa ne sukayi a baya bayan nan kuma duka a wajen tashi, wanda a cewarsu akwai shakku akan sahihancin wadannan jiragen kirar Amurka.

Baya ga kasar China,  kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines, shi ma ya sanar da dakatar da zurga zurga ta jiragensa samfarin Boeing 737 MAX 8, har sai an gama bincike bayan hatsarin na jiya.

Kamfanin Ethiopian Airlines, nada irin wandanan jiragen guda hudu, a yayin da yayi odar wasu 29.

Su ma kasashen Koriya ta kudu da Mongolia, da Indonusia sun dau irin wannan matakin na dakatar da sufirin irin wadanan jiragen.

Kasar Afrika ta kudu ita ma a cikin wata sanarwa ta dakatar da amfani da samfarin jirgin irinsa guda da take dashi, kamar yadda hukumar sufurin jiragen sama ta kasar ta sanar a cikin wata sanarwa duk a cewarta tana da yakini akan sahihancin jirgin.

Wasu Kamfanonin da suka dakatar da aikin da jiragen samfarin Boeing 737 MAX 8, sun hada da kamfanin Cayman Airways na tsibirin Caïmans, da Singapoor.

Rasha ta ce tana bibiyar lamarin, a yayin da wasu kamfanonin suka ce su kam ba zasu dakatar da aiki da jiragen ba da sauri haka.

Tuni dai Hannayan jari na kamfanin Boing sun fadi da kashi 12% a baya bayan nan.

Kamfanonin sun hada dana Air Italy, Icelandair, da kuma na Amurka Southwest da American Airlines, da Air Canada da Turkish Airlines, sun ce su kam jiragensu na ci gaba da aiki, kuma suna aiki da sharudan aiki da jiragen.

Jirgin kirar kamfanin Boing na Amurka samfarin 737 MAX 8, shi ne wani jirgi da ya fi samun karbuwa a kasuwannin duniya.

 

Tags