Mar 14, 2019 16:35 UTC
  • An Aike Da Bakaken Akwatuna Na Jirgin Ethipoia Da Ya Fadi Zuwa Faransa

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Ethiopia ya aike da bakaken akwatuna biyu masu nadar bayanai na jirgin da ya fadi zuwa kasar Faransa.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a yau Alhamis kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines ya aike da na'urori biyu masu nadar bayanai a cikin jirgin kamfanion da ya fadi zuwa birnin Paris domin yin bincike a kan musababbin faduwar jirgin.

Wanann na zuwa ne bayan da Jamus ta ki amincewa ta dauki nauyin gudanar da binciken na'urorin biyu, bisa dalilin cewa ba za ta iya karanta bayanan da na'urorin suka nada ba.

Ita kuwa a nata bangaren kasar Amurka cewa ta yi na'urorin sun bugu sosai, mai yiwuwa hakan ya iya shafar wasu bayanan da ake bukatar samu.