Mar 14, 2019 16:42 UTC
  • Venezuela: An Koma Bakin Aiki Bayan Dawowar Wutar Lantarki A Yawan Yankuna

A yau Alhamis an koma baki ayyuka a kasar Venezuela, bayan daukewar wutar lantarki na kusan mako guda a kasar, wanda ya yi sanadiyyar tsayawar harkoki da dama a kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, bisa umarnin da shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayar, a yau an koma bakin ayyuka  akasar, bayan da ayyuka da dama suka tsaya cak sanadiyayr daukewar wutar lantarki babu zato babu tsammania  fadin kasar baki daya.

A ranar Alhamis 7 ga wannan wata na Maris ne dai wutar lantarki ta dauke a dukkanin kasar Venezuela, inda ministan wuta na kasar ya ce an yi kutse ne a cikin tsarin da ke tafiyar da harkokin wutar ta hanyar yanar gizo, inda aka lalata tsarin, wanda hakan ya yi sanadiyarr daukewar wutar.

Shuga Maduro dai ya zargi Amurka da hannu kai tsayea  cikin lamarin, kamar yadda kuma ya bayyana hakan da cewa daya ne daga cikin hanyoyin yakin da Amurka ta shelanta kan kasar ta Venezuela da nufin rusa ta, inda ya ce kamar yadda suka yi nasara a yanzua kan a yakin wutar lantarki, aka za su yi nasara  a kanta a sauran fagage.