Mar 16, 2019 05:22 UTC
  • Rasha:'Yan Ta'adda Na Shirye-Shiryen Kai Hari Da Makamai Masu Guba A Idlib

Ma'aikatar harakokin wajen Rasha ta sanar a jiya juma'a cewa 'yan ta'addar kungiyar Tahriru Sham na shirye-shiryen kai hari da makamai masu guba a birnin Idlib na kasar Siriya

Cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya juma'a, ma'aikatar harakokin wajen Rasha ta ce 'yan ta'addar na kokarin kai wannan hari ne bisa goyon bayan dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

Sanarwar ta ce kasar Rasha na sa ido sosai kan abinda ke abinda ke faruwa a birnin Idlib da kuma yankunan kasar ta Siriya.

A watan Maris din shekarar 2013 ne bisa goyon bayan Amurka da Birtaniya aka kafa Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD daga kasar Turkiya wadanda kuma manufarsu shi ne ci gaba da bayar da kariya kan 'yan ta'adda a wuraren da suka karkashin mamayar 'yan ta'adda a Siriya