Mar 16, 2019 05:23 UTC
  • MDD TaYi Allah Wadai Kan Harin Ta'addancin Da Aka Kaiwa Musulmi A New Zeland

Saktare janar na MDD cikin wani bayani da ya fitar ya yi allah wadai kan harin ta'addancin da aka kaiwa musulmi a kasar New zeland sannan ya ce ya zama wajibi a hada kai wajen yakar masu kyamar musulmi a Duniya

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto babban saktaren Majalisar Dinkin Duniya  Antonio Guterres cikin wani bayyani da ya fitar a shafin sadarwarsa na  Twitter na cewa shakka babu abinda ya faru a kasar New-zeland abu ne dake tayar da hankali, mutunan da ba su ji ba su gani ba, kuma ba tare da sun aikata ko wani irin laifi ba, suna cikin bauta a tarar da su a kashe su, mun yi allah wadai da wannan ta'addanci.

Yayin da yake mika ta'aziyarsa kan iyalan wadanda harin ya ritsa da su, Guterres ya ce wajibi ne a yau da kulun mu hada kai wurin guda domin yakar masu kyamar musulmi da addinai da kuma duk wani na'in kyama da ta'assubanci.

A safiyar jiya juma'a ne wasu 'yan ta'adda dauke da makamai suka kai hari cikin masallatai Lainuwud da Annor dake gefen yankin Christchurc dake kasar New-Zeland, inda suka kashe mutum 49 tare da jikkata wasu 50 na daban.

A yayin da yake Allah wadai da kai harin, Firai ministan kasar New-Zeland Jacinda Ardern ya bayyana harin, da ta'addanci da kuma wanda ba a taba ganin irinsa a kasar ba.