Shugabar Kasar Brazil, Rouseff, Na Fuskantar Barazanar Tsigewa A Majalisar Kasar
(last modified Tue, 12 Apr 2016 18:11:31 GMT )
Apr 12, 2016 18:11 UTC
  • Shugabar Kasar Brazil,  Rouseff, Na Fuskantar Barazanar Tsigewa A Majalisar Kasar

Rahotanni daga kasar Brazil suna nuni da cewa shugabar kasar Dilma Rouseff na fuskantar barazanar rasa kujerarta bayan da kwamitin musammman na majalisar dokokin kasar ya kada kuri'ar amincewa da batun tsige ta da 'yan adawa suka gabatar.

An cimma wannan matsaya ne bayan kuri'ar da aka kada a kwamitin musamman din kan batun tsige shugabar inda aka samu kuri'u 38 masu goyon baya a kan 27 da suka ki amincewa da hakan.

Rahotanni sun ce a halin yanzu dai za a sake gabatar da batun don samun cikakkiyar kuri'a a zauren majalisar dokokin inda matukar aka samu kashi biyu bisa uku to za a ci gaba da batun tsige shugabar.

'Yan adawan dai suna zargin shugaba Rouseff da yi wa tattalin arzikin kasar ta'annuti bugu da kari kuma kan zargin rashawa da cin hanci da ake zarginta da shi, zargin da shugabar ta musanta; tana mai bayyana hakan a matsayin kokarin yi mata juyin mulki.

A ranar Asabar mai zuwa ne ake sa ran za a kada cikakkiyar kuri'ar a majalisar mai mutane 513.