Myammar : Anyiwa Fursuna 63 Ahuwa
(last modified Sun, 17 Apr 2016 10:48:53 GMT )
Apr 17, 2016 10:48 UTC
  • Shugaban kasar Myammar, Htin Kyaw
    Shugaban kasar Myammar, Htin Kyaw

A wani mataki na hada kan al'ummar kasa, sabon shugaban kasar Myammar Htin Kyaw yayiwa wasu firsina siyasa 63 ahuwa, kamar yadda wata kungiya dake taimakwa mutanen da ake tsare da a gidajen yari ta tabbatar.

Wannan dai na zuwa a daidai lokacin da ake bukukuwan shiga sabuwa shekara a wannan kasa.

hakan dai ya tabbatar da matakin da sabuwar gwamnatin kasar ta dauka na kawo sauyi bayan mulkin soji da tsawan shekaru da dama.

tun da farko dai gwamnatin kasar ta wallafa a shafin ta na facebook cewa zatayi ahuwa ga firsina 83 da ake tsare da su a gidajen kurkuku daban-daban na kasar ta yadda za'a samu walwala da jin dadi da hadin kan al'umma a wannan kasa.