Goyon bayan Shgaban Kasar Rasha ga Gwamnatin Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i4054-goyon_bayan_shgaban_kasar_rasha_ga_gwamnatin_siriya
Shugaban Kasar Rasha ya bayyana cewa zai ci gaba da taimakon Gwamnatin Siriya a yakin da take yi da ta'addanci
(last modified 2018-08-22T06:58:09+00:00 )
Apr 18, 2016 12:41 UTC
  • Goyon bayan Shgaban Kasar Rasha ga Gwamnatin Siriya

Shugaban Kasar Rasha ya bayyana cewa zai ci gaba da taimakon Gwamnatin Siriya a yakin da take yi da ta'addanci

A wani sako da ya aikewa Shugaban kasar Siriya a yau Litinin, Shugaban Kasar Rasha Viladimin Putin ya kara jadadda goyon bayan sa ga Shugaban kasar Siriya Bashard Al-Assad tare da bayyana cewa Gwamnatin Masco za ta ci gaba da taimakawa Gwamnatin Damuscus a yakin da take yi da ta'addanci a kasar, har ila yau Shugaba Putin ya meka sakon barka da salla ga Gwamnati da kuma Al'ummar Siriya dangane da ranar zagayowar ranar samun 'yancin kai da ake kira da sallar Jala'a.

Har ila yau Shugaban kasar ta Rasha ya tabbatar da cewa babu gudu babu ja da baya a goyon bayan da suke baiwa Gwamnatin Siriya tare da kare duk wani yunkuri na masu son raba kasar

Putin ya kara da cewa ci gaba da karfafa alaka tsakanin kasashen biyu, shi ne zai tabbatar da kyakkyawar alaka gami da kare manufofin kasashen Siriya da Rasha.

A ranar 17 ga watan Avrilu ne Al'ummar kasar Siriyan suka gudanar da bikin samun 'yancin kai karo na 70 wato ranar da suka kori Sojojin kasar Faransa daga cikin kasar inda suka kiran wannan biki da Sallar Jala'a.