Rasha: ISiS nada manbobi dubu 33 a Kasashe Siriya da Iraki
https://parstoday.ir/ha/news/world-i4474-rasha_isis_nada_manbobi_dubu_33_a_kasashe_siriya_da_iraki
Kungiyar Leken asirin Sojin Rasha ta sanar da cewa kungiyar ISIS nada manbobi dubu 33 a kasashen Siriya da Rasha.
(last modified 2018-08-22T06:58:11+00:00 )
Apr 28, 2016 00:46 UTC
  • Rasha: ISiS nada manbobi dubu 33 a Kasashe Siriya da Iraki

Kungiyar Leken asirin Sojin Rasha ta sanar da cewa kungiyar ISIS nada manbobi dubu 33 a kasashen Siriya da Rasha.

Tashar Telbijin din Almayadin wacce ke watsa shirye-shiryanta daga kasar Lobnon ta habarta cewa bisa rahoton da kungiyar leken asirin Sojin Rasha ta fitar kungiyar ISiS na da mayaka kimanin dubu 19 a kasar Iraki sannan kuma a kasar Siriya dubu 14.

Rahoton ya ce kungiyar ta ISiS na amfani da kanana gami da manyan makamai da suka hada da tankokin yaki, manyan bindigogi, makamai masu lizzami da kuma makamai masu kakkabo jiragen yaki.

har ila yau Rahoton ya ce kungiyar ta ISIS nada mayaka kimanin 4500 a yankin tsakiyar Asiya da suke amfani da rikicin kabilanci ko na addini domin samun kare manufofinsu. a yankin Afirka kuwa kungiyar nada shiri na dogon lokaci a yankin, inda ta yi kokarin janyo hanakalin matasa na wasu kasashen Larabawa dubu 4 a kasar Libiya.

Rahoton ya yi galgadin cewa matukar kungiyoyin 'yan ta'addar ISIS da na AlQa'ida suka hade kansu a yankin Afirka to ba shakka za su jefa yanayin tsaron yakin cikin hadari.

A bangaren kasashen Turai kuwa, rahoton ya ce tun shekaru 4 da suka gabata fiye da 'yan ta'adda 800 ne suka shiga kasar Jamus, lamarin da ya sanya al'amuran tsaron kasashen shiga cikin hadari.