Biritaniya : Karon Farko, Musulmi Ya Zama Magajin Garin London
A Biritaniya an samu musulmi na farko daya lashe zaben magajin garin London.
Sadiq Khan dan shekaru 45 a duniya ya lashe zaben Magajin garin London a karkashin babbar jam'iyyar adawar Biritaniya ta Labour.
Jin kada bayan lashe zaben shugaban jam'iyyar Labour, Jeremy Corbyn ya aike da sakon taya murna ta shafin sa twitter, ga Sadiq Khan, yana mai cewa ''ina mai jiran ganin na fara aiki tare da kai domin maida London gari na kowa da kowa''
Wannan sakamakon zaben dai zai kara wa shugaban jam'iyyar Labour, Jeremy Corbyn kwarin-gwiwa.
Tun da farko dai wasu sunyi hasashen cewa jam'iyyar za ta yi mummunar faduwa kasancewar koma bayan data fuskanta a wasu sassan kasar a yayin zaben jihohi dana kananan hukumomi na ran Alhamis data gabata.
Mayan ayukan dake gaban sabon magajin garin na Londan sun hada da magance matsalar tsadar gidaje, sifiri, da kuma gurbatar yanayi.
ments inabordables, transports saturés et pollution.