Shugaban Majalisar Brazil Ya Soke Yunkurin Tsige Dilma Rousseff
Shugaban Majalisar Brazil ya soke yunkurin tsige shugabar kasar Uwal gida Dilma Rousseff da majalisar dokokin kasar ta amunce dashi a ranar 17 ga watan Afrilu daya gabata.
Tuni dai wannan matakin na ba zata da Mr Waldir Maranhao ya dauka ya hadassa babban rudani a wannan kasa, a daidai lokacion da ake shirin gabatar da shirin tsige shugabar kasar Roussef.
A cikin wata sanarwa daya aike wa manema labarai Mr Maranhao ya ce akwai wasu hanyoyin da majalisar zata sake biya domin a kai ga sake gabatar da yunkurin neman tsaige Roussef, kuma a cewar sa dukkan matakan na a hannun majalisar datijan kasar.
Mr Maranhao shi ne dai wanda ya maye gurbin wacen shugaban majalisar wakilan kasar Eduardo Cunha a makon daya gabata, bayan kotun kolin kasar ta dakatar dashi bisa zargin cin hanci, kuma shi ne wanda ya fara gabatar da shirin tsige shugabar kasar Uwal gida Dilma Roussef.
Ana dai zargin shugabar kasar ta Brazil da badakalar cin hanci da yin almundahana da kudaden gwamnati a yayin yakin neman zabenta shekaru biyu da suka gabata, saidai Rousseff ta ci gaba da musanta haka a tsawon lokacin da yan adawa suka kwashe suna kiran a tsigeta .