Halakar Bakin Haure A Tekun Kasar Turkiyya
Wani karamin jirgin ruwa da ke dauke da bakin haure 28 ya kife a cikin teku a kan hanyarsa ta zuwa Tsibirin Lesbos na kasar Girka daga kasar Turkiyya.
Jami’an tsaron bakin teku da suke gudanar da ceto a gabar tekun kasar Turkiyya sun kai dauki wa bakin haure, inda suka yi nasarar kubutar da mutane hudu, amma bakin haure 24 sun halaka a cikin tekun.
Har ila yau wani kwale-kwale da ke dauke da bakin haure 11 ya nutse a tekun Izmir na kasar Turkiyya, inda jami’an gudanar da ceto a bakin tekun suka samu nasarar kubutar da mutane uku.
Wannan hatsari na kifewar jiragen ruwa a teku da suke kokarin fataucin bakin haure zuwa kasashen yammacin Turai ya zo ne a daidai lokacin da waziriyar kasar Jamus Engila Markel take gudanar da zaman tattaunawa da mahukuntan kasar Turkiyya kan tsaurara matakan dakile yawan bakin haure da suke kokarin shiga cikin kasashen na Turai musamman ta hanyar teku da hakan ke kai ga hasarar rayukansu.