Bukatar Karfafa Alaka Tsakanin Kungiyar Tarayyar Afrika Da Majalisar Dinkin Duniya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i5134-bukatar_karfafa_alaka_tsakanin_kungiyar_tarayyar_afrika_da_majalisar_dinkin_duniya
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci karfafa alaka tsakaninta da kungiyar tarayyar Afrika da nufin bunkasa harkar tsaro da sulhu a nahiyar ta Afrika.
(last modified 2018-08-22T06:58:16+00:00 )
May 13, 2016 06:32 UTC
  • Bukatar Karfafa Alaka Tsakanin Kungiyar Tarayyar Afrika Da Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci karfafa alaka tsakaninta da kungiyar tarayyar Afrika da nufin bunkasa harkar tsaro da sulhu a nahiyar ta Afrika.

A zaman taron da ya gudana tsakanin mambobin Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyar tarayyar Afrika a jiya Alhamis: Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Jan Eliasson ya jaddada bukatar samun fahimtar juna da gudanar da aiki tare a tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Trayyar Afrika musamman a fagen bunkasa shirin wanzar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar ta Afrika.

Jan Eliasson ya jaddada cewa; Batun neman wanzar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afrika yana daga cikin manyan manufofin da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya a gaba, don haka kungiyar tarayyar Afrika ita ce kungiya mafi muhimmanci da Majalisar zata hada kai da ita domin ganin an cimma burin da aka sanya a gaba.