Girka : Yawan Bakin Hauren Dake Kwarara Turai Ya Ragu
Bayan samun ragowar kashi 90% na yawan bakin haure dake isa Girka domin shiga Turai ya ragu a watan Afrilu, da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta sanar, 'yan sanda a kasar ta Girka tabbatar da ragowar kwararar bakin hauren matuka.
'Yan sanda Girka sun kawo ba'a samu wasi sabbin bakin haure da suka shiga kasar ba tun daga ranar Asabar data gabata.
Wannan dai baya rasa nasaba da yarjejeniyar da kasashen Belgium da Turkiyya suka cimma domin takaita kwararar bakin hauren zuwa Turai.
koda yake bayanai sun nuna har yanzu dai sauren rina a kaba akan yunkurin dakatar da kwararen bakin hauren, kasancewar a baya bayan nan ma a cafke wasu bakin hauren kimanin 50 dake kokarin shiga kasar ta hanyar kasa.