Wani Jirgin Saman Fasinjan Kasar Masar Ya Bace A yau Alhamis
Kamfanin jiragen samar kasar Masar (Egypt Air) ya sanar da bacewar wani jirgin saman fasinjar da ke dauke da mutane 69 a cikinsa a kan hanyarsa ta zuwa birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar din daga birnin Paris, babban birnin kasar Faransa.
A wata sanarwa da kamfanin jiragen saman na Masar ya watsa a shafinta na Tweeter ya ce jirginsa mai lamba MS804 mai dauke da fasinjoji 59 da ma'aikata 10 ya bace daga idanuwan na'urorin radar da suke sanya ido kansa. Sanarwar ta kara da cewa jirgin ya bace ne a lokacin da yake kan ruwan Mediterraniya, kimanin mile 10 kafin ya shiga sararin samaniyar kasar Masar din.
Sanarwar ta kara da cewa a halin yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan hakikanin abin da ya faru da jirgin.
A watan Oktoban shekarar bara ma dai wani wani jirgin fasinjan kasar Rasha yayi hatsari a kasar Masar din inda mutane 224 da suke cikinsa suka mutu. Ana zargin 'yan kungiyar Da'esh ne dai suka tarwatsa jirgin ta hanyar sanya bomb a cikinsa.