Hari kan Matatar Man dake kalkashin kungiyar ISIS A Siriya.
Jiragen yakin kasar Rasha sun ruwa bama-bamai kan wata Matamar Man fetur dake kalakashin kungiyar ISIS a kasar Siriya.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar a wannan Laraba cewa Dakarun tsaron kasar dake gudanar da aiyukan yaki da ta'addaci a kasar Siriya sun kai hari da jiragen yaki samfari S-34 kan wata Matatar Man fatur da 'yan ta'adda ke amfani da ita wajen tace danyan mai a wani yanki dake kalkashin ikonsu na jihar Haska, lamarin da ya yi sanadiyar rugurguza matatar.
Ma'aikatar tsaron Rashan ta tabbatar da cewa Dakarun saman kasar za su ci gaba da kai hare-hare kan duk wata Ma'aikata ko kamfani da 'yan ta'addar ke amfani da shi wajen samar da kudaden shiga har sai sun ruguza tattalin arzikin 'yan ta'addar, yanzu haka Dakarun saman na Rasha na ci gaba da kai hare-hare kan jihar Kalamun.
Rahoton ya ce bayan ruwan bama-baman da Jiragen yakin Rashan suka kai kan Matatan Man ta yankin Haska, Matatar ta kama da wuta,kuma an ji kara mai karfi na tashi daga kamfanin Matatan man.