Kasashen Musulmi Da Dama Sun Fara Azumta Watan Ramadana
Yau Litinin kasashen musulmi da dama sun fara gudanar da azumin watan mai alfarma, sakamakon ganin jaririn watan na Ramadana a daren jiya.
Azumin watan ramadana shi ne rukuni na hudu na addinin Islama, kuma ya tanadi kame baki daga duk wani ci da sha, da kusantar iyali da wasu miyagun halaye ko dabi'o'i.
A ranar Lahadi mahukunta a Saudiyya sun bayyana cewa sakamakon ganin jaririn watan Musulmai a kasar sun tashi da azumin a wannan Litinin.
Kuma akwai kasashe da dama na Musulmai da suka bayyana haka, ciki har da Najeriya, Nijar, da Kamaru.
Azumin dai na bana ya zo ne a daidai lokacin da kasashen musulmi da dama irin su Syria, Yemen, yankin Zirin gaza na Palestine, Irak, Najeriya dama Nijar, da Libya ke fuskantar matsalar 'yan ta'ada na takfiriya dake ikirarin jihadi da sunan musulinci.
A nan jamhuriya Musulinci ta Iran a gobe ne ake sa ran fara gudanar da Azumin, yayin da yanzu haka ake shirye-shiryen hangen jinjirin watan.