Najeriya : Amnesty Ta Zargi Sojoji Da Kisan 'Yan Biafra
https://parstoday.ir/ha/news/world-i6517-najeriya_amnesty_ta_zargi_sojoji_da_kisan_'yan_biafra
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da kisan 'yan biafra a bikin tunawa da fafutukar kafa Jamhuriyar Biafra a garin Onitsha, a watan jiya.
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 10, 2016 05:58 UTC
  • Najeriya : Amnesty Ta Zargi Sojoji Da Kisan 'Yan Biafra

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da kisan 'yan biafra a bikin tunawa da fafutukar kafa Jamhuriyar Biafra a garin Onitsha, a watan jiya.

A rahoto data fitar yau Juma'a Amnesty ta ce sojojin sun kashe akalla mutum 40 sannan aka jikkata fiye da 50 a gabani da kuma bayan zanga-zangar goyan bayan 'yan a ware na Biafra.

Amnesty ta ce akwai mutanen da aka harba da bindiga a baya, wanda yake nuna cewa sun nemi tserewa ne aka harbe su.

Saidai tuni rundunar sojin Nigeria ta yi watsi da rahoton na Amnesty International tane mai cewa jami'an tsaron sun yi aikinsu ne na tabbatar da zaman lafiya, a yayin zanga-zanga ta neman tada zaune tsaye.