Faransa : An Dauki Matakai Gabanin Gasar Turai
Jun 10, 2016 06:09 UTC
Shugaba Francois Hollande na Faransa ya ce, kasar ta dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin kare lafiyar al'umma da tabbatar da walwalarsu a yayin da kasar ke gab da bude gasar cin kofin kasashen Turai da kasar ke daukar bakunci.
A yau Juma'a ne dai ake bude gasar da kasar ke daukan bakunci har na tsawan wata guda.
An jibge jami'an tsaro kimanin dubu 90 don saboda kaucewa yiwuwar kaddamar da hare-haren ta'addanci a kasar.
Tuni dai dubban ‘yan kallo daga sassan duniya suka isa Faransa, inda a wannan Juma'a Faransa mai masaukin baki, za ta bude fage da Romania a filin wasa na Stade De France da ke birnin Paris.
Tags