Ba Zamu Kara Karbar Tallafin EU Ba, Inji MSF
https://parstoday.ir/ha/news/world-i6880-ba_zamu_kara_karbar_tallafin_eu_ba_inji_msf
Kungiyar likitoci marar iyaka ta MSF ta ce daga yanzu ba zata kara karbar wani tallafi ba daga kungiyar tarrayya Turai.
(last modified 2018-08-22T06:58:27+00:00 )
Jun 18, 2016 01:19 UTC
  • Ba Zamu Kara Karbar Tallafin EU Ba, Inji MSF

Kungiyar likitoci marar iyaka ta MSF ta ce daga yanzu ba zata kara karbar wani tallafi ba daga kungiyar tarrayya Turai.

MSF, ta ce daga yanzu ta daina karbar duk wani tallafi daga kungiyar ta Eu ko rassan ta ko kuma kasashe mambobin ta.

Wannan matakin a cewar sakatare janar na kungiyar ta MSF, Jérôme Oberreit domin kalubalantar siyasar kasashen 28 mambobin (EU) din akan bakin haure.

Da yake bayyana hakan a wani taron manema labarai Jiya a Brussels M. Jérôme Oberreit ya bayyana cewa wannan matakin zai fara aiki nan take kuma a duk rasunan kungiyar a fadin duniya.

Yau kusa da watanni uku kenan da kungiyar (EU) da kasar Turkiyya suka cimma matsaya akan hana bakin haure kwararar zuwa Turai ta kasar Turkiyya.

Yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma ta tanadi maida duk sabbin bakin hauren har ma da masu neman mafaka a Turan zuwa kasar ta Turkiyya, wace EU zata zubama $ bilyan uku kafin karshen shekara 2018 domin ta girke 'yan gudun hijira Syria a cikin kasar ta.

Alkalumen da MDD ta fitar sun nuna cewa sama da bakin haure miliyan daya ne suka shiga turai a bara kawai.