(EU) Na Goyan Bayan Tattaunawar Sulhu Tsakanin Palestinu Da Israi'la
https://parstoday.ir/ha/news/world-i6994-(eu)_na_goyan_bayan_tattaunawar_sulhu_tsakanin_palestinu_da_israi'la
kungiyar tarraya turai ta (EU) ta ce tana bada cikaken goyan bayan ta ga faransa kan yunkurin ta na farfado da tattaunawar zamen lafiya tsakanin Palestinu da Israi'la.
(last modified 2018-08-22T06:58:28+00:00 )
Jun 20, 2016 13:21 UTC
  • (EU) Na Goyan Bayan Tattaunawar Sulhu Tsakanin Palestinu Da Israi'la

kungiyar tarraya turai ta (EU) ta ce tana bada cikaken goyan bayan ta ga faransa kan yunkurin ta na farfado da tattaunawar zamen lafiya tsakanin Palestinu da Israi'la.

kungiyar ta (EU) dake sa ran yin ganawa ta daban-daban da shugaban Palestinawa Mahmoud Abbas da kuma na Hahudawa Isra'ila a wannan mako ta ce zata taimakawa faransa matuka a wajen farfado da tattauanwar.

 

A wani taro ne da suka gudanar a Luxembourg, ministocin harkokin wajen kungiyar ta EU suka sanar da hakan.

 

A karshen wannan shekara ce faransa ke sa ran shirya wani taron kasa da kasa domin farfado da tattaunawar zamen lafiya tsakanin bangarorin biyu.

 

A ranar 3 ga watan ne ministoci da wakilai talatin daga kasashen larabawa da na yammaci da MDD da kungiyar EU suka halarci taron kaddamar da shirin a birnin paris na Faransa, duk da cewa ba'a gayyaci Palestinu da Isra'ilar ba bata ma maraba da shirin.