Paparoma da Kirill na bukatar a kare kiristoci
(last modified Sat, 13 Feb 2016 11:21:59 GMT )
Feb 13, 2016 11:21 UTC
  •   Kirill da Paparoma Francis
    Kirill da Paparoma Francis

Tuni dai Paparoma Francis ya isa kasar Mexico domin ci gaba da ziyarsa

Shugaban darikar katolika ta duniya, Paparoma Francis da shugaban Kristocin Orthodox na Rasha Kirill, sun bukaci kasashen duniya da su kare lafiyar al’ummar Krista da ke fuskantar barazana a yankin gabas ta tsakiya.

Shugabanin dai na magana ne akan tashe tashen hankula da ake fama da su a yankin musamen na kungiyar (IS).

Shugabanin sun ce, an lalata kauyuka da biranen mabiya addinin Kirista da dama a gabas ta tsakiya da arewacin Afrika tare da kaskanta wuraren ibadunsu.