An Ceto sama da 'Yan gudun Hijra dubu biyu A Bahrum
(last modified Fri, 24 Jun 2016 18:08:12 GMT )
Jun 24, 2016 18:08 UTC
  • An Ceto sama da 'Yan gudun Hijra dubu biyu A Bahrum

Jami'an tsaron ruwan Italiya sun sanar da ceto bakin haure sama da dubu biyu a tekun Meditarinia

Jaridar Le figaro ta kasar Faransa ta nakalto Dakarun tsaron ruwan Italiya na cewa A yau juma'a sun ceto bakin haure sama da 2000 a tekun Meditarinia inda kuma a aka yi la'akari da wadnda aka ceto jiya Alkhamis, sama da bakin haure dubu bakwai da 100 ne Dakarun ruwan suka ceto cikin sa'o'i 24 kacal.

Dakarun tsaron Ruwan Italiyan sun ce mafi yawan bakin hauren sun fito daga kasar Libiya ne a kan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai, inda masu safarar Mutanan ke amfani da yanayin ruwa gami da yanayin iska wajen yawaita shigar da bakin hauren zuwa kasar Italiya.

Bisa alkaluman da Gwamnatin Italiya ta fitar kimanin bakin haure dubu 60 ne suka isa kasar daga farkon watan Avrilun wannan shekara da muke ciki.