Yakin Ruwan Sanyi Tsakanin Rasha Da Nato
Nato: Ba mu Son Komawa Zuwa Lokacin Yakin Ruwan Sanyi
Babban Kwamandan Sojan Kungiyar Tsaro ta Nato, ya ce; Ko kadan ba su son komawa lokacin yakin ruwan sanyi.
A yau asabar ne kwamandan rundunar tsaro ta Nato janar Philip Breedlove ya ce; Kungiyarsu ba ta da sha'awar sake komawa cikin yakin ruwan Sanyi. Kwamandan na kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Naton, dai ya fadi haka ne a kasar Jamus a wani taron manema labaru.
Janar Phillip wanda ya kaucewa ambaton sunan kasar Rasha kai tsaye, ya kara da cewa; matakan da suke dauka na kare kai ne.
A jiya juma'a ne dai piraminsitan kasar Rasha Dmitry Mededov ya ce: matakan da kungiyar ta Nato ta ke dauka akan Rasha suna cike da nuna kiyayya, abinda ya sake maida mu cikin yakin ruwan sanyi.