Birtaniya Ta Kafa Kwamitin Ficewa Daga Turai.
Jun 27, 2016 14:30 UTC
Pira ministan Birtaniya Ya sanar da kafa Kwamitin Bin diddigin Ficewa daga tarayyar turai.
David Cameroon ya fada a yau litinin cewa majalisar zartarwa ta amince da kafa wani kwamiti wanda zai bi diddigin ficewar kasar daga cikin tarayyar turai.
Cameroon ya ci gaba da cewa; Bisa la'akari da cewa sakamakon zaben raba gardama a kasar, na ficewa daga tarayyar turai, an kafa kwamiti da wakilci daga ma'aikatun kasuwanci da baitul-mali da ma'aikatar harkokin waje domin bin diddigin ficewa daga tarayyar ta turai.
Bugu da kari, Dadiv Cameroon ya ce zai halarci taron kungiyar tarayyar turai din wanda za a yi a gobe, inda a can ma zai tattauna batun ficewar kasar tasa.
Tags