Argentina : An Nemi Messi Ya yi Hakuri
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7345-argentina_an_nemi_messi_ya_yi_hakuri
Shugaban Argentina ya nemi dan wasan kwallon kasarsa, wato Lionel Messi da yayi hakuri ya ci gaba da murzawa kasar leda.
(last modified 2018-08-22T11:28:30+00:00 )
Jun 28, 2016 06:23 UTC
  • Argentina : An Nemi Messi Ya yi Hakuri

Shugaban Argentina ya nemi dan wasan kwallon kasarsa, wato Lionel Messi da yayi hakuri ya ci gaba da murzawa kasar leda.

Messi dai ya sanar da yin ritaya daga murza leda a kasashen duniya bayan da ya kasa zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga a wasan da Chile ta dokr Argentina, kana ta dauki kofi gasar Copa America.

A wata hira ta wayar tarho jiya shugaba Mauricio Macri, ya nemi Messi da yayi hakuri ya ci gaba da bugawa kasar kwallo, kuma ya bar biye fade-fade jama'a.

Shi ma shahararen tsohon dan wasan kasar Dieggo Maradona ya yi irin wannan kira ga Messi.

Wannan dai shi ne karo na hudu da tawagar kwallon kafar kasar ke shan kashi a wasan karshe a cikin shekara tara, lamarin da ya janyo suka ba kadan ba ga dan wasan kasar Lionel Messi.