Taron Farko Na EU, Bayan Ficewar Biritaniya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7348-taron_farko_na_eu_bayan_ficewar_biritaniya
Yau Talata, shugabanni da gwamnatoci na kasahen kungiyar tarayya turai ke taro domin cilastawa Biritaniya gaggauta ficewa daga cikin kungiyar ta EU.
(last modified 2018-08-22T11:28:30+00:00 )
Jun 28, 2016 06:23 UTC
  • Taron Farko Na EU, Bayan Ficewar Biritaniya

Yau Talata, shugabanni da gwamnatoci na kasahen kungiyar tarayya turai ke taro domin cilastawa Biritaniya gaggauta ficewa daga cikin kungiyar ta EU.

Wannan dai shi ne taro farko na kasashen mambobin kungiyar tun bayan zabin al'ummar Biritaniya na ficewa daga cikin kungiyar.

 

Taron dai na yau wanda firaministan Biritaniya David Cameron zai halarta nada nufin cilastawa kasar kaddamar da shirin ta na barin kungiyar ba tare da bata lokaci ba.

 

Jan- kafa da Biritaniya ke nunawa kan fara shirin janyewar ta a cewar kasashen 27+1 babbar barazana ce ga kasuwanni.

 

kasashen turan zasu kuma tattauna batutuwa da dama da suka shafi makomar kungiyar nan gaba da nifin yin riga kafi kan hakan ya zama abin koyi ga sauran kasashen kungiyar.

 

A halin da ake ciki kasashe mafiya tattalin arziki na kungiyar ta EU, sunyi fatali da duk wata tattaunawa da mahukuntan na Londan, mudin basu fara shirye-shiryen janyewa daga cikin kungiyar ba.